http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/manchester-united-ta-kai-matsayi-na-hudu-a-jerin-klub--klub-din-ingila/7039192.html
Wani dan wasan kwallon kafa ya kirkiri jin ciwo na da gan-gan domin ya ba abokin wasansa dama ya yi bude baki sabili da azumin da ya ya ke yi, wannan abu ya faru ne a ranar Asabar a filin da ake buga wasa tsakanin klub din Fiorentina da Milan, inda aka ga dan wasa Luka Ranieri ya kirkiri jin ciwo na karya domin ya ba Sofyan Amrabat damar shan ruwa bayan azumi. A gefe guda kuma dan damben zamani Anthony Joshua, dan Najeriya mazaunin Ingila, ya ce Laura Woods, wata mace mai gabatar da...