http://www.hausawglwpwzr4svrerazwxt7mqpcw3hfoxp5r7jjrkttqc3qrs5syid.onion/a/rikicin-sudan-wata-sabuwar-yarjejeniyar-tsagaita-wuta-za-ta-fara-aiki/7104979.html
Washington DC — Volker Perthes ya shaida wa taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya cewa, "Wannan wani ci gaba ne na marhabin, ko da yake an ci gaba da gwabza fada da yunkurin sojoji har zuwa yanzu, duk da kudurin da bangarorin biyu suka yi na ba za su ci gaba da fada ba kafin tsagaita wutar ta fara aiki." Perthes ya yi tafiya zuwa New York daga Port Sudan. Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da wasu ma'aikatanta da ayyukanta na wani dan lokaci zuwa birnin na Red Sea, bayan kazamin...